'Yan gudun hijirar Sudan na fuskantar babban hadari' -Human Rights Watch

'Yan gudun hijirar Sudan na fuskantar babban hadari' -Human Rights Watch

Mayakan Fano da ke da da tungar su a jihar Amhara, na daya daga cikin kungiyoyi da dama da ke fafatawa da gwamnatin tarayya tun bayan da ta sha alwashin murkushe dakarun sa kai a watan Afrilun 2023.

 A watan Yuni ne wa'adin dokar ta baci da gwamnati ta kafa a yankin Amhara mai mutane miliyan 23, ta kare a watan Yuni amma ana ci gaba da tashe tashen hankula, inda a watan Satumba aka jibge dakaru masu tarin yawa na gwamnatin tarayya.

Yankin dai ya yi iyaka da Sudan, wanda shi kansa ke fama da yakin basasa tsakanin dakarun sa kai da dakarun gwamnati tun a shekara ta 2023.

Wani sansanin dakarun kasar Sudan Wani sansanin dakarun kasar Sudan AP - Sam Mednick

Mataimakiyar darektan Afirka ta kungiyar kare hakkin bil'adama ta Human (HRW) Laetitia Bader ta ce "'Yan gudun hijirar Sudan da ke Habasha sun shafe sama da shekara guda suna fuskantar cin zarafi.

 Kungiyar ta HRW ta ce a cikin wani rahoto da ta fitar ta ce "masu dauke da makamai da mayakan sa-kai na yankin sun yi kisan kai, da duka, da kwasar ganima, da garkuwa da mutane.

Wasu daga cikin yankunan da yakin Sudan ya shafa Wasu daga cikin yankunan da yakin Sudan ya shafa AFP - -

Rahoton na dada bayana cewa ana ci gaba da cin zarafi mutane tun watan Yunin 2023.

Kungiyar kare hakkin bil adama ta kuma zargi gwamnatin Habasha da girke dakarun ta a wuraren da ake fama da rikicin cikin gida kafin barkewar yaki a Sudan amma duk da haka tana samar da “iyakantaccen tsaro”.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)