'Yan gudun hijiran Jamhuriyar Congo na ci gaba da kwarara zuwa Burundi

'Yan gudun hijiran Jamhuriyar Congo na ci gaba da kwarara zuwa Burundi

Majalissar Ɗinkin Duniya ta nuna fargaba bayan yan tawayen M23 da ke samun goyon bayan Rwanda a gabashin Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Congo, sun kama ikon manyan garuruwan kasar da suka hada da Goma da Bukavu.

Babban birnin Bukavu mai kimanin mutane miliyan daya dake iyaka  da Rwanda, tazarar kilomita 50 ne tsakanin sa da Burundi, wanda ke ɗauke da mafi yawancin 'yan gudun hijirar da suka tserewa yaƙe-yaƙe tun farkon shekara ta 2000, kamar yadda wakiliyar hukumar 'yan gudun hijira ta Burundi, Brigitte Mukanga-Eno ta sanar .

Bugu-da ƙari a hira da manema labarai a Bujumbura, uwargidan ta ce a yan kawanakin da suka gabata, sun karbi yan gudun hijira kimanin dubu 30, yayin da wasu ke ci gaba da kwararo wa daga yankunan da ke fama da tashin hankali.

Mai magana da yawun sojin kasar, ya ce akwai fargabar wannan rikici ya rikide zuwa makamancin  yakin daya faru a Congo a  shekarar 1998 zuwa 2003, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama, tare da jefa dubbai cikin mawuyacin hali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)