Tunisia da ke arewacin Afirka da ma makwabciyarta Libya, sun zama muhimman wuraren da bakin haure ke amfani da su a kokarin su na neman tsallakawa zuwa Turai .
Galibi bakin haure daga wasu sassan nahiyar, wadanda ke fuskantar hadarin balaguron teku da fatan samun ingantacciyar rayuwa a Turai, Farid Ben Jha, mai magana da yawun masu shigar da kara na yankin gabashin Monastir da Mahdia, ya ce wadanda suka tsira daga hatsarin jirgin na baya-bayan nan sun shaida wa hukumomi cewa jirgin nasu ya kife bayan ya tashi a daren ranar Talata.
Mutanen sun taso ne daga birnin Sfax da ke gabar teku zuwa kudu, babban tashar tashi da bakin haure zuwa Italia. A cewar mai magana da yawun kotun, dukkan fasinjoji 42 sun fito ne daga kasashen yankin kudu da hamadar sahara, ciki har da mata takwas. Wasu daga cikin wadanda aka ceto sun fito ne daga kasashen Kamaru da Senegal da kuma Guinea.
A kowace shekara, dubun dubatar mutane suna ƙoƙari su tsallaka Tekun Bahar Rum. Italia, wacce tsibirin Lampedusa ke da tazarar kilomita 150 (mil 90) daga Tunisia, galibi ita ce tashar jiragen ruwa ta farko. Tun daga farkon wannan shekara, kungiyar kare hakkin dan adam ta Tunusia FTDES ta kidaya "tsakanin 'yan cirani 600 zuwa 700" da suka mutu da kuma bacewarsu sakamakon kifewar jiragen ruwa a kusa da kasar Tunisia, bayan da bakin haure sama da 1,300 suka mutu ko kuma suka bace a shekarar 2023.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI