Jawabin ya mayar da hankali ne a kan wasu matsalolin da suka addabi Afirka, suka kuma hana ta ci gaba tare da tabo batutuwa irin su yakin Afghanistan da rikici tsakanin Isra'ila da Falasdinu da kuma yunwa a duniya. Kwanaki 11 bayan wannan jawabi aka hallaka shugaba Sankara da wasu daga cikin mukarabansa, sojan da ya maye gurbin Sankara, babban aminin sa kuma mataimakinsa Blaise Compaore.
Tsohon Shugaban mulkin sojin Burkina Faso,Kyaftin Thomas Sankara AFP - ALEXANDER JOEBincike da kuma sheidu yan lokuta da kisan Thomas Sankara sun tabbatar da zargin da ake na cewa Blaise Compaore wanda babban aboki ne ga Sankara ne ya hallaka shi.
Thomas Sankara © Muigwithania/Wikimedia, CC BY-NCAn dai dauki dogon lokaci kafin daga bisali kotu ta yanke hukunci na daurin rai da rai ga tsohon Shugaban kasar ta Burkina Faso Blaise Compaore wanda ke gudun hijira a Cote D’Ivoire,mutumen da alkalai masu kare shi suka dau alkawalin daukaka kara duk da cewa Blaise Compaore ya shugabanci Burkina Faso tsawon shekaru sama da 20.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI