Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara, ASP Yazid Abubakar, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya kuma bayar da tabbacin cewa kwamishinan ‘yan sandan jihar ya umarci jami’an rundunar da su kai dauki domin ceto wadanda lamarin ya shafa.
Wani mazaunin garin na Moriki ya shaida wa manema labarai cewa ‘yan bindigar sun futuni al’umma, kuma bayan da tun da farko sun yi garkuwa da wasu mutanen yankin.
Sannan ‘Yan bindigar sun bayyana cewa sun kai harin ne bayanda Kwamandan ƴan sakai ya kashe shanunsu a yayin da suka bi gida-gida suna zabar mutane, sannan kuma suka yanke za a biya su Naira miliyan 50 a matsayin kudin fansa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI