'Yan bindiga sun hallaka fararen hula 8 a Togo

'Yan bindiga sun hallaka fararen hula 8 a Togo

Majiyoyi daga  wasu mazauna kauyukan sun shaida cewa  ‘yan bindigar sun zo ne a cikin daren juma’a wayewa safiyar asabar inda bayan sunyi kutse a wani gida  da aka tsugunar da ‘yan gudun hijra  suka yi wa mai gidan da sauran mutane 7 kisan gilla.

Majiya ta kara da cewa a wanan karon  ‘yan bindigar sun hari kauyen  Malgabangou  ne an kuma kiyasta akalla mutane 8 sun mutu.

Wanan shi ne karo na biyu a cikin makwani biyu da yankin ya fuskanci harin ‘yan bindiga.

Kawo yanzu dai babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin, sai dai a baya kungiyar mayaka masu ikrarin Jihadi ta JNIM ta sha kai hare hare a baya a wanan yankin.

Tun daga shekara 2021, kauyukan dake yammacin gunduma Kpendjal a kasar ta Togo ke fuskanta hare haren ‘yan bindiga masu dauke da makamai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)