Mayakan sunyi garkuwa da malamin ne a kusa da iyakar kasar Mauritania a hanyar sa ta dawowa daga wani taron wa’azi inda suka yi ta canza masa wurare daban-daban domin azabtar dashi kamar yadda wani dan uwan sa daya nemi a sakaya sunan sa ya shaida wa kampanin dillancin labarai na AFP
Kafin rasuwar marigayin, ya kasance shugaba a kungiyar Tijjaniya daya daga cikin manyan rassa na sufanci dake yammacin Africa
Tun a shekarar 2012 ne kasar mali ke fuskantar matsalolin ta’addanci da rashin kwanciyar hankiali,wannan yasa shuwagabannin sojin kasar suka yanke alakar dake tsakanin su da paransa data rene su tare da kulla sabon alakar soji da Rasha
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI