'Yan adawar Guinea sun nemi sojoji su mika mulki daga nan zuwa watan Janairu

'Yan adawar Guinea sun nemi sojoji su mika mulki daga nan zuwa watan Janairu

Gwamnatin mulkin sojan da ta kwace mulki a shekarar 2021, ta yi alkawarin mika mulki ga farar hula a 2022, bayan tattaunawa da kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka, sai dai har yanzu babu alamun shirya zabe, lamarin da ya tayar da hankalin jama'a.

‘Yan kasar dai sun gudanar da zanga-zangar adawa da yadda hukumomi da sauran mukarraban shugaban mulkin soji Mamady Doumbouya ke tafiyar da kasar tun bayan hawansa mulki, abinda ya kai ga kazamin artabu da jami’an tsaro a wasu yankuna.

A cikin watan Yuli ne hukumomin rikon kwarya na Guinea suka gabatar da daftarin sabon kundin tsarin mulkin da zai bai wa Doumbouya damar shiga zaben shugaban kasa mai zuwa.

Har yanzu dai ba a sanya ranar da za a gudanar da zaben raba gardama kan kundin tsarin mulkin kasar da aka yi alkawari ba, wanda a cewarsu zai zama mafarin shirye-shiryen yadda za a gudanar da zaben.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)