'Yan adawar Angola sun gudanar da zanga-zanga a birnin Luanda

'Yan adawar Angola sun gudanar da zanga-zanga a birnin Luanda

Jama’a a yayin wannan taro na ta furta kalamai marar dadi ga Shugaban kasar inda suke cewa  "Lourenço fita", "Mutane na mutuwa saboda yunwa", Waɗannan wasu daga cikin take-taken da za a iya karantawa jiya a titunan Luanda yayin zanga-zangar lumana, wadda ta tattaro dubban 'yan Angola.

Joao Lourenço shi ne ke mulkin kasa ta biyu a Afirka mai arzikin man fetur tun shekara ta 2017, kuma sau da yawa 'yan adawa na zarginsa da mulkin kama karya.

Sakatare Janar na Unita, Alvaro Chikwamanga, ya bayyana cewa zanga-zangar na da nufin nuna rashin amincewa da "mummunan shugabanci na Joao Lourenço".

"Mutanen Angola na fama da yunwa, yara suna fama da rashin abinci mai gina jiki da kuma cin abinci daga kwandon shara yayin da kasarmu ke da arzikin albarkatu," in ji shi.

A cikin taron, Elisabeth Ana Bela, wata daliba 'yar shekara 24, ta ce ta shiga harkar ne saboda "yunwa na da yawa a kasarmu, dole ne al'amura su canza.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)