Shugabannin jam’iyyun adawar da suka hada da tsohon shugaban ƙasar Joseph Kabila da tsoffin ƴan takarar shugabancin ƙasar Martin Fayulu da Moise Katumbi ne suka yi kira ga magoya bayan nasu da su gudanar da zanga-zangar adawa da Shirin shugaba Felix Tshisekedi.
A watan da ya gabata ne, Mista Tshisekedi ya sanar da shirin kafa wani kwamitin ƙasa a shekara mai zuwa wanda zai rubuta sabon ƙundin tsarin mulkin ƙasar da ke tsakiyar Afirka, lamarin da ya taɗa hanhalin ƴan adawa da ke zargin wani ƙoƙari na tsawaita wa'adin shugabancin ƙasar.
Cikin wata sanarwar haɗin guiwa da suka fitar ranar Laraba, gamayyar jam’iyyun adawa, ta hannun kakakin jam’iyyar Kabila, Shadary Ramazani, sun ce matakin, shirin zagon ƙasa ne ga demokradiya.
Shugaba Tshisekedi ya sha sukar ƙundin tsarin mulkin da ƙasar ke amfani da shi a halin yanzu, wanda aka amince da shi ta hanyar kuri'ar raba gardama a shekarar 2006, yana mai cewa, bai dace da zamani ba, inda ƴan adawa ke nuna damuwarsu cewa shugaban ƙasar na ƙoƙarin sauya wa'adin shugabancin ƙasar na shekaru biyar – biyar sau biyu, don ci gaba da zama a madafun mulki.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI