'Yan adawa a Kamaru sun bukaci yi wa dokokin zaɓe gyaran fuska

'Yan adawa a Kamaru sun bukaci yi wa dokokin zaɓe gyaran fuska

Ɗan majalisar dokoki Hon Koupit Adamou daga jam’iyyar adawa ta UDC, yana daga cikin waɗanda suka jagoranci gabatar da wannan buƙata, ga kuma abin da ya shaida wa RFI.

"Lura da irin yadda muka gabatar da buƙatar a wannan karo, ko shakka babu a wannan lokacin saƙon zai isa ga shugaban ƙasa", in ji Adamou.

Ya ce, sun rubuta wa shugaban ne a hukumance, tare da yaƙinin cewa zai isa hannunsa, kuma alhaki ne da ya rataya a wuyansa don amincewa ko ƙin amincewa da buƙatun da aka gabatar masa.

"Abin da muka gabatar wa shugaban, sakamakon jituwa ce da aka cimma a tsakanin ‘yan siyasa da ke cikin ƙawancenmu, saboda haka, matuƙar ana buƙatar cimma fahintar juna, ya zama wajibi a samu goyon gwamnati", a cewar sa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)