Yajin aikin malaman jami'o'i ka iya rikidewa zuwa zanga-zanga a Kamaru

Yajin aikin malaman jami'o'i ka iya rikidewa zuwa zanga-zanga a Kamaru

An samu rahoton taruwar jama’a a kusa da jami’o’I da kuma gine-ginen gwamnati, musamman a birane irin su Yaounde.

Abin da ake fargaba shine, idan har daliban kasar suka goyi bayan wannan yajin aikin, to akwai yuwuwar barkewar zanga-zangar da za ta iya haifar da arangama da jami’na tsaro.

An tsaurara matakan tsaro da kuma takaita zirga-zirgar ababen hawa, musamman a kusa da wuraren da ake fargabar barkewar zanga-zanga.

A watan Oktoban bara ne, malaman jami’o’in kasar suka yi barazanar tafiya yajin aiki na gargadi, matsawar gwamnatin Kamaru ta gaza biya musu bukatunsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)