Shugaban Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya Laftanal Janar Farouk Yahaya ya bayyana cewa, sun gamsu da kayan tsaron da suka saya daga Turkiyya.
Yahaya ya gana da Jakadan Turkiyya a Abuja Hidayet Bayraktar a helkwatar rundunar sojin kasa da ke Birnin Tarayyar.
A yayin ganawar an tattauna kan yadda za a habaka alakar aiyukan soji tsakanin Najeriya da Turkiyya.
A jawabin da Yahaya ya yi a yayin ganawar ya kuma ce, baje-kolin kayan tsaro da aka gudanar a Turkiyya ta IDEF 2021 ta samu nasara sosai, sun yi ganawa mai ma'ana da shugabannin sojin Turkiyya.
Shugaban Sojojin kasa na Najeriyar ya kara da cewa, suna son habaka alakar soji da Najeriya.
Ya ce, "Ya zuwa yanzu mun gamsu da kayan tsaron da muka saya daga Turkiyya kuma muka yi amfani da su. Muna aiyukan sake sayen wasu kayayyakin."
Jakadan Turkiyya Bayraktar kuma ya ja hankali kan yadda Turkiyya ta ke bayar da muhimmanci wajen habaka alakar soji da Najeriya, kuma za su samar da wani bigire da zai kara kulla alaka tsakanin Najeriya da masana'antun kayan tsaro na Turkiyya.