Rahotanni daga kasar sun ce, jami'an hukumar na gabatar da tambayoyi kan tsohon gwamnan na Kogi.
Yayin da rahotanni ke cewa hukumar yaki da cin hancin ta cafke shi, wasu bayanan na cewa ya kai kansa ofishin hukumar ne tare da lauyoyinsa
A zaman sauraron karar da aka yi ranar 14 ga Nuwamba, EFCc ta nemi a daga zaman zuwa 27 ga Nuwamba, game da korage-korafen da ta shiga kan Yahaya Bello.
A watan Afrilu ne, EFCC ta ayyana neman tsohon gwamnan Kogin ruwa a jallo, bayan da bayanai suka ce ya ki amsa gayyatar da hukumar ta yi masa.
Jami'an hukumar a wancan lokacin sun kai samame gidan Yahaya Bello da ke Abuja domin cafke shi, amma hakan ya gagara.
Rahotanni sun ce, EFCC ta shirya cafke shi tare da hadin gwiwar hukumar tsaron farin kaya ta DSS, lokacin da gwamnan jihar Kogi na yanzu Usman Ododo, ya isa gidan nasa domin bashi kariya.
Daga bisani gwamnan ya fice daga gidan nasa, kuma rahotanni sun tabbatar da cewa tare suka fice, abin da ya tilastawa jami'an tsaron da ke neman kamashi bude wuta.
Tun daga lokacin da al'amarin ya faru a ranar 17 ga Afrilun 2024, ba a sake ganin Yahaya Bello a bainar jama'a ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI