Majalisar ɗinkin Duniya, ta bayyana matuƙar damuwa da yadda ɓangarori masu rikici da juna a Libya ke ɗaukar sabbin mayaƙa a baya-bayan nan, lamarin da ta ce na matsayin barazana ga ƙoƙarin da ake na shawo kan rikicin ƙasar musamman hararar juna da aka samu bayan korar shugaban babban bankin ƙasar.
Da ta ke jawabi a taron kwamitin tsaro na Majalisar, Stephanie Koury mataimakiyar shugabar shirin wanzar da zaman lafiya a Libya, ta ce ƙasar na fuskantar ƙaruwar farraƙa tsakanin ɓangarori masu rikici da juna cikin watanni 2 da suka gabata a kusan dukkan matakai.
Wata sanarwa da kwamitin tsaron na majalisar ya fitar, ya bayyana matakan da mayaƙan na Libya ke ɗauka wajen bajekolin makaman da suka mallaka a matsayin lamarin da majalisar ba za ta lamunta ba.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, matakin da suke ɗauka na barazana tare da cutar da rayuwar fararen hular da ke kewaye da su.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI