Gambari wanda ya taba rike mukamin ministan harkokin wajen Najeriya ya ce manyan kasashen duniya ayau sun mayar da Afirka dandalin fafatawa a tsakanin su domin cimma muradunsu ta fannin siyasa da tattalin arziki da kuma tsaro, ya yin da nahiyar bata amfanar komai daga wannan yunkuri.
Farfesa Gambari da Aung San Suu Kyi lokaci da ya rike mukamin jakadan majalisar dinkin duniya na musaman akan Myanmar (Photo : AFP)Farfesa Gambari ya ce wannan manyan kasashe da yanzu haka ke ci gaba da girke sojojin su a sassa daban daban na Afirka, na amfani da su wajen cimma muradun su na hakar ma'adinai, sayar da kayayyakin yaki da kuma mamaye harkokin kasuwanci da zuba jari, abinda ke mayar da wasu kasashen tamkar bayi wadanda ba su da karfin fada aji.
Masanin ya ce wadannan manyan kasashe na duniya irin su Amurka da Rasha da China da Jamus da Faransa da Birtaniya da kuma India yau sun mallaki wasu yankuna inda suka girke sojojin su da sunan taimakawa kasashen Afirka dake fama da matsalar tsaro, amma kuma abin takaici sai ga shi a wannan lokaci ne tashe tashen hankula suka yi kamari a nahiyar baki daya.
Tsohon Jakadan ya ce duk da matsalolin da nahiyar Afirka ke fuskanta, tana da makoma mai kyau saboda arzikin matasan da Allah ya mata da kuma yawan al'ummar da ta zarce biliyan guda.
Ibrahim Gambari. (Photo : Reuters)Gambari ya ce amfani da wannan arziki na yawan jama'a zai bai wa nahiyar damar bunkasa harkokin ci gaban ta a bangarori da dama da suka hada da tattalin arziki da makamashi da kuma fasahar zamani.
Tsohon ministan ya ce ya zama wajibi Afirka ta tashi tsaye wajen ganin an dama da ita a bangarori da dama na shata ko kuma rubuta sabbbin dokoki da harkokin ci gaban duniya baki daya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI