Wutar lantarkin Najeriya ta ɗauke gaba ɗaya

Wutar lantarkin Najeriya ta ɗauke gaba ɗaya

Wannan ɗaukewa ita ce karo na farko a shekarar 2025, amma karo na 13 cikin watanni 13 da suka gabata.

Rahotanni sun nuna cewa wutar lantarki ta fara raguwa daga megawat 2,111.01 da misalin ƙarfe 2 na rana.

Daga bisani ta sauka zuwa megawat 390.20 da misalin ƙarfe 3 na rana.

A shekarar da ta gabata, layin samar da wutar lantarkin ya lalace sau 12, wanda hakan ya jefa miliyoyin ’yan Najeriya cikin duhu tare da kawo cikas ga tattalin arziƙi da rayuwar yau da kullum.

Wannan lalacewar na zuwa ne kwanaki 11 kacal da shiga sabuwar shekarar 2025.

Hakan ya sake nuna yadda matsalar rashin ingantaccen tsarin samar da wutar lantarki ke ta’azzara a ƙasar.

Al’ummar Najeriya dai na ci gaba da fuskantar ƙalubale a fannin samar da wutar lantarki, wanda ke da matuƙar tasiri a harkokin kasuwanci, masana’antu, da rayuwar yau da kullum.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)