William Ruto na fatan ganin an cimma tsagaita bude wuta tsakanin M23 da DRCongo

William Ruto na fatan ganin an cimma tsagaita bude wuta tsakanin M23 da DRCongo

Shugaban na Kenya William Ruto na magana ne a taron shugabannin kudanḉi da gaɓashin Afirka da aka gudanar a Tanzania domin kokarin lalubo hanyar fita daga rikicin da ya ɓarke a gaɓashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo fiye da shekaru uku da kuma kara ruruwa a 'yan makonnin nan.

Shugaban kasar Kenya, William Ruto Shugaban kasar Kenya, William Ruto © william Ruto Twitter

An kira taron na hadin gwiwa na ƙasashe 8 na kungiyar ƙasashen gaɓashin Afrika EAC da ƙasashe 16 na ƙungiyar raya ƙasashen ƙudanḉin Afirka (SADC) bayan da sojojin kasar Rwanda suka ƙwace Goma, ɓabban birnin lardin Kivu ta Arewa cikin ɗan kankkanin lokaci.

  Wannan taro ya gudana a Dar es Salaam a gaban shugaban kasar Rwanda Paul Kagame yayin da takwaransa na Congo Félix Tshisekedi ke halartar taron ta bidiyo.

Yankin Lushagala, a garin Goma,na DRCongo Yankin Lushagala, a garin Goma,na DRCongo AFP - TONY KARUMBA

    Shugabannin kasashen Kenya, Somalia, Uganda, Zambia da Zimbabwe sun halarci bude taron,wanda William Ruto ta jadada cewa “a tsagaita bude wuta nan take ita ce hanya ɗaya tilo da za a samar da yanayin tattaunawa mai ma’ana da kuma aiwatar da ḉikakkiyar yarjejeniyar zaman lafiya.”

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)