WHO za ta aike da tawaga ta musamman Rwanda bayan ɓullar cutar Marburg

WHO za ta aike da tawaga ta musamman Rwanda bayan ɓullar cutar Marburg

Shugabar hukumar ta WHO shiyyar Afrika Dr Matshidiso Moeti ta bayyana cewa nan kusa za ta aike da tawagar ƙwararrun jami’ai zuwa ƙasar ta Rwanda daga ofishinta da ke Kenya.

Ma’aikatar lafiyar Rwanda ta ce tuni ta bi diddigin kusan dukkanin mutanen 121 da suka yi mu’amala da waɗanda cutar ta kashe inda yanzu haka aka killace su a wani yunƙuri na daƙile barazanar cutar mai haɗari.

Cutar ta Marburg da ke cikin dangin Ebola, na sahun cutukan da wasu kan yaɗawa wasu ta hanyar mu’amalar da ta ƙunshi ko dai musabuha da za ta kai ga shafar jiki ko kuma musayar lumfashi.

Masana kiwon lafiya na bayar da shawarwarin killace dukkanin wanda ake fargabar ya kamu da wannan cuta don daƙile barazanar yaɗuwarta.

Zuwa yanzu cutar ta fantsama zuwa sassa 7 cikin yankuna 30 na Rwanda ciki har da Kigali fadar gwamnatin ƙasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)