WHO za ta aikawa Guinea da allurar riga-kafin Ebola

WHO za ta aikawa Guinea da allurar riga-kafin Ebola

Hukumar Lafiya ta Duniya wato WHO za ta aikewa Guinea allura rigakafin Ebola guda dubu 11.

Daraktan WHO a Afirka Matshidiso Moeti, ya bayyana cewa za'a aike da ma'aikata 100 da doz din allura rigakafin Ebola dubu 11 a ranar Lahadi 21 ga watan Febrairu.

Da yake bayyana cewa za a fara aiki da alluarar a ranar 22 ga watan Febrairu ya kara da cewa ana shirin siyar doz dubu 8 da 600 daga Amurka.

Moeti, ya kara da cewa tun daga kasashen dake da iyaka da Giunea da kuma ma dukkanin kasashen Sahran Afrika ya kamata su dauki matakai.

Daga cikin kasashen dake da makwobtaka da Giune a yammacin Afrika sun hada da Senegal, Mali, da Ivory Coast, da Liberia, da Saliyo da Guinea Bissau.

 


News Source:   ()