WHO ta yi gargadi game da jabun alluran riga-kafin Corona a Indiya da Afirka

WHO ta yi gargadi game da jabun alluran riga-kafin Corona a Indiya da Afirka

Hukumar Kula da Lafiya ta Duniya (WHO) ta bayyana cewa, an gano jabun alluran riga-kafin Corona a Indiya da Afirka.

WHO ta yi gargadi kan a tattare alluran daga kasuwanni wadanda suna barazana sosai ga lafiyar duniya.

WHO ta bayyana cewa, Cibiyar Samar da Allurai da ke Indiya ta kama jabun allurar riga-kafin da kamfanin AstraZeneca ya samar mai suna "Covishield" a watannin Yuli da Agusta.

Baya ga Indiya an kuma gano jabun alluran riga-kafin a Uganda da ke Afirka.

Ya zuwa yanzu an yi amfani da allurar riga-kafin Corona ta Covishield guda miliyan 486 a Indiya.

A watan Mayu ne Indiya ta fuskanci zango na 2 na yaduwar Corona wanda hakan ya sanya ta hana fitar da allurar har nan da karshen shekara don biyan bukatar cikin gida.

An raba allurar riga-kafi ta Covishield a kasashen Afirka da Asiya da dama.

Hukumar Samar da Allurai ta Indiya ba ta ce komai ba game da batun.


News Source:   ()