WHO ta tabbatar da ɓullar cutar zazzaɓin Marburg a Tanzania

WHO ta tabbatar da ɓullar cutar zazzaɓin Marburg a Tanzania

Cutar ta zazzaɓin Marburg da ke da haɗarin gaske duba da yadda ta ke da saurin ruɓanya da kashi 88 , ta na daga rukunin cutukan Ebola da ke yaɗuwa daga mutum zuwa mutum bayan da tun farko aka ɗakko ta daga jikin jemagen wadda aka ga ɓullarta a lokuta da dama cikin yankin na gabashin Afrika.

WHO ta ce ta samu sahihan rahotannin da ke nuna cewa cutar ta Murburg ta ɓulla a yankin Kagera na Tanzania tun a ranar 10 ga watan da muke ciki na Janairu, kuma akwai fargabar ta iya fantsama zuwa wasu yankuna.

Wasu daga cikin alamun wannan cuta kamar yadda WHO ke sanarwa sun ƙunshi ciwon kai da masassara sai ciwon baya kana gudawa sannan amai da kuma sagewar gaɓoɓi baya ga zubar jini daga jiki.

Yanzu haka akwai gwajin aƙalla mutum biyu da ake dakon fitar sakamakonsu daga ɗakin gwaji daga asibitin Tanzania.

Can a Tanzania WHO ta ce akwai mutane aƙalla mutane 66 da ynzu haka ke ɗauke da ita baya ga wasu mutane 15 da ta hallaka tun bayan ɓullarta a ranar 20 ga watan Disamba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)