WHO ta tabbatar da mutuwar mutane 50 sakamakon wata cuta a Congo

WHO ta tabbatar da mutuwar mutane 50 sakamakon wata cuta a Congo

Sanarwar da WHO ta fitar ta ce daga ranar 16 ga watan da muke ciki na Fabarairu zuwa yanzu mutane 431 suka harbu da nau’in cutukan biyu ciki har da 53 da suka mutu, cutukan da aka samu ɓullarsu a wasu ƙauyuka biyu masu nisa da juna da ke lardin Equateur.

Congo wadda girmanta ke kaiwa kwatankwacin ilahirin girman ƙasashen yammacin Turai, na ganin ɓullar cutuka kala-kala inda ko a bara aka ga ɓullar wata nau’in cuta da ta hallaka tarin mutane gabanin gano cewa zazzaɓin cizon sauro ne ya zo da wani yanayi.

A wannan karon WHO ta ce cutar tana yaɗuwa cikin gaggawa fiye da hasashe a ƴan kwanakin nan, lamarin da kakakin hukumar Tarik Jasarevic ke cewa babbar barazana ce ga lafiyar jama’a.

Hukumar ta ce har zuwa yanzu ba a gano dalilin da ke haddasa cutar ba, a wani yanayi da ƙauyukan da aka ga ɓullar cutar ke fama da durƙushewar sashen lafiya.

Tun farko a ranar 13 ga watan nan ne aka samu ɓullar cutar daga ƙauyen Bomate na gundumar lafiya ta Basankusu da ke lardin na Equateur  da zuwa yanzu ta hallaka mutane 45 daga cikin mutane 419 da suka harbu, kuma kusan rabi na adadin sun mutu ne cikin ƙasa da sa’o’i 48.

WHO ta ce tana ci gaba da bincike kan cutar da nufin ɗaukar matakan daƙile yaɗuwarta.

Wasu daga cikin alamomin cutar a cewar WHO sun ƙunshi zafin jiki da kuma amai da gudawa, kuma galibi ta kan hallaka mutane lokaci ƙanƙani bayan kamuwa da ita.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)