WHO ta ayyana wata baƙuwar cuta a Congo a matsayin annoba

WHO ta ayyana wata baƙuwar cuta a Congo a matsayin annoba

A wani sabon rahoto da hukumar lafiya ta duniyar ta fitar a daren Lahadin da ta gabata,  ta ce aƙalla mutane 406 ne aka tabbatar sun kamu da baƙuwar cutar daga ranar 24 ga watan Oktoba zuwa 5 ga watan Disamba, inda mutane 31 suka rasa rayukansu.

Alamomin cutar da har yanzu ba’a san musabbabinta ba, sun haɗa da zazzaɓi, ciwon kai, mura da ciwon jiki.

Cutar ta fi yaɗuwa ne a yankin Panzi na kudu maso yammacin Kwango.

A cewar WHO, yawancin waɗanda suka kamu da cutar ƙananan yara ne ƴan kasa da shekaru 5, yayin da wasu kuma mutane ne da basa samun abinci mai gina jiki.

Sanarwar ta ƙara da cewa dama can yankin na fama da cutar zazzaɓin cizon sauro wanda ake kyautata zaton nada alaƙa da sabuwar cutar, sai dai masana sun bayyana cewa akwai yiwuwar sama da cuta 1 ce ta haddasa ɓullar baƙuwar cutar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)