A karkashin shirin ta na samar da alluran riga-kafin Corona (Covid-19) ga kasashe matalauta, Hukumar Kula da Lafiya ta Duniya (WHO) ta aika da alluran riga-kafin cutar zuwa kasashen Afirka 44.
Sanarwar da aka fitar ta shafin Twitter na Ofishin Hukumar a yankin Afirka ta ce, ya zuwa yanzu an kai allurai miliyan 7,7 zuwa yankunan da su ke da hstari sosai.
Sanarwar ta ce, "A karkashin shirin COVAX na samar da riga-kafin Corona da dukkan duniya, an kaiwa kasashen Afirka 44 alluran."
WHO ta ce, an fara yin alluran a kasashen Afirka 32 daga cikin 44.
Sanarwar ta rawaito gargadin da Cibiyar Yaki da Cututtuka ta Afirka ta yi na cewa, rikicin riga-kafin Corona da ake samu a kasashen yamma na iya shafar nahiyar Afirka.
Ya zuwa yanzu mutane miliyan 4 da dubu 168 Corona ta kama a Afirka, kuma sama da dubu 111,000 sun rasa rayukansu.