WHO na duba yiwuwar sanya dokar ta ɓaci kan cutar ƙyandar biri a Congo

WHO na duba yiwuwar sanya dokar ta ɓaci kan cutar ƙyandar biri a Congo

A jawabinsa gaban taron manyan jami’an WHO da ya gudana a birnin Geneva shugaban hukumar Dr Tedros Adhanom Ghebreyesus ya buƙaci ganawar ƙwararru daga ƙasashen duniya don tattaunawa kan yadda za a shawo kan cutar ta ƙyandar biri a Congo da kuma yadda ta ke bazuwa ƙasashen makwabta, lamarin da ya bayyana da mai tayar da hankula.

A cewar shugaban na WHO kwamitin kar ta kwana na WHO zai yi zama da ƙwararrun don samun shawarwari tare da sanin ko akwai buƙatar sanya dokar ta ɓacin ƙasa da ƙasa akan cutar ko akasin haka, wanda zai bayar da damar ɗaukar matakan yaƙar bazuwar cutar mai haɗari.

A shekarar 1970 aka fara gano cutar ta ƙyandar biri a jamhuriyyar demokradiyyar Congo wadda akan samu daga jikin dabbobi amma kuma ta kan yaɗu daga jikin mutum zuwa mutum, ko a watan Mayun shekarar 2022 anga bazuwarta a ƙasashe daban-daban har zuwa cikin shekarar 2023 lamarin da ya tilasta WHO sanya dokar ta ɓaci akanta.

Tun daga shekarar 2023 Congo ke ci gaba da ganin ɓullar nau’ika daban-daban na wannan cuta ta ƙyandar biri.

Daga ranar 11 ga watan Yuli kawo yanzu WHO ta ce an samu mutane dubu 11 da ke ɗauke da cutar baya ga wasu 445 da suka mutu galibinsu ƙananan yara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)