WHO: Kasa da kaso 2 na alluran riga-kafin da aka yi a duniya aka yi a Afirka

WHO: Kasa da kaso 2 na alluran riga-kafin da aka yi a duniya aka yi a Afirka

Hukumar Kula da Lafiya ta Duniya (WHO) ta bayyana cewa, kasa da kaso 2 na alluran riga-kafin Corona (Covid-19) da aka yi a duniya aka yi a Afirka.

Daraktar WHO a Afirka Dr. Matshidiso Moeti ta zanta da manema labarai inda ta bayyana cewa, a kasashen Afirka da dama ba a yi allurar riga-kafin cutar Corona yadda ya kamata ba.

Ta ce, a kasashen Afirka da dama ba a samu wata nasara sosai a aiyukan yaki da cutar Corona da ake yi, kuma daga cikin kunshin allurai dubu 700 da aka yi a duniya baki daya, kasa da kaso 2 aka yi a nahiyar Afirka.

Moeti ta ci gaba da cewa, "Matsalolin rashin wajen ajiya da kuma samun allurar na hana mutane da dama gasa samun riga-kafin a nahiyar."

Moeti ta ce, an kai allurai sama da miliyan 30 zuwa Afirka, amma miliyan 13 kawai aka yiwa jama'a.

A Afirka cutar Corona ta yi ajalin mutane dubu 115, ta kama mutane miliyan 4,500 inda kusan mutane miliyan 4 sun warke.

 


News Source:   ()