Daraktar Hukumar Lafiya ta DUniya (WHO) ta Afirka Dr. Matshidiso Moeti ta bayyana cewar annobar Corona ta sake tabarbarar da yanayin da mutane miliyan 200 da ba sa samun isasshen abinci a nahiyar suke ciki.
A taron manema labarai da Moeti ta gabatar ta hanyar sadarwar 'Teleconference' ta ce akwai bukatar gaggawa ta abinci a nahiyar Afirka, wadanda ba sa samun isasshen abinci ba su da garkuwar jiki mai karfi.
Ta ce har yanzu akwai mutane miliyan 200 da ba sa samun isasshen abinci a Afirka, kuma Covid-19 ta sake jefa su cikin mummunan yanayi.
Sama da mutane dubu 70 annobar Corona ta kama a Afirka inda aka samu rasa rayuka sama dubu 2,500.