WHO: Corona na yaduwa sosai a kasashen Afirka

WHO: Corona na yaduwa sosai a kasashen Afirka

Yaduwar cutar Corona a nahiyar Afirka ya karu sosai inda ya kafa tarihi tun bayan bullar annobar.

Daraktar Hukumar Kula da Lafiya (WHO) a Afirka Matshidiso Moeti ta gudanar da taron gaggawa tare da manema labarai inda ta ce, yaduwar cutar a karo na 2 ya haura girmamar da ya yi a makon da ya gabata inda a wannan makon ya karu da mutane dubu 251.

Moeti ta ja hankali kan yadda makonni 7 a jere kenan cutar na kara yaduwa.

Ta ce, "Har yanzu Afirka ba ta fuskanci munin yanayin cutar ba."

Daraktar ta WHO a Afirka Moeiti ta kuma cewa, a kasashen nahiyar nau'in Delta na cutar Corona na ci gaba da yaduwa musamman a kasashe 10.

Moeti ta yi nuni da cewa, kaso 1,6 na alluran riga-kafin da aka yi a duniya ne kawai aka yi a Afirka inda ya zuwa aka yi wa mutane miliyan 16 allurar a nahiyar.


News Source:   ()