A nahiyar Afirka ana bukatar alluran riga-kafin Corona miliyan 20 cikin gaggawa.
Daraktar WHO ta Afirka Dakta Matshidiso Moeti ta shaida cewa, nan da watan Satumba ana sa ran yi wa kaso 10 na jama'ar Afirka allurar riga-kafin.
Moeti ta kara da cewa, "Afirka na bukatar riga-kafi a yau. Dakatar da yin allurar na iya janyo dagulewar al'amura a Afirka."
Moeti ta kara da cewa, Afirka na bukatar alluran riga-kafin Corona cikin gaggawa, kuma ya yi wuri a bayyana yiwuwar samun kamuwa da cutar a zango na 3 a Afirka.