WHO: Afirka ba ta shirya tunkarar yaduwar Corona a karo na 3 ba

WHO: Afirka ba ta shirya tunkarar yaduwar Corona a karo na 3 ba

An shaida cewa, asibitoci manya da kanana da ke Afirka ba su shirya dauka da magance yaduwar cutar Corona (Covid-19) a karo na 3 ba.

Daraktar Hukumar Kula da Lafiya ta Duniya (WHO) a Afirka Dr. Matshidiso Moeti ta sanar da cewa, ana ci gaba da fuskantar barazanar yaduwar Corona a karo na 3 a Afirka inda ta gargadi mahukunta game da hakan.

Ta ce, "Har yanzu asibitoci manya da kanana da ke Afirka ba za su iya daukar marasa lafiya da yawa da ake kai musu."

Moeti ta kuma yi kira da a samarwa da ma'aikatan lafiya kayan aiki masu inganci sosai.

 


News Source:   ()