Wannan bincike na zuwa ne a dai dai lokacin da hukumar samar da abicnin ta majalisar ɗinkin duniya ke fuskantar matsaloli wajen ciyar da miliyoyin mutanen da yaƙi ya ɗaiɗaita a Sudan, waɗanda ke fuskantar ƙarancin abinci mafi muni a cikin shekaru da dama.
A matsayin wani ɓangare na binciken, masu bincike na ƙoƙarin gano ko waɗannan jami’an da ake tuhuma sun yi ƙoƙarin ɓoye irin rawar da rundunar sojin Sudan ta taka ta dakile agaji a yayin wannan yaki da aka shafe watannni 16 ana gwabzawa tsakanin da rundunar RSF.
Ɗaya daga cikin waɗanda ake binciken shi ne mataimakin shugaban hukumar abincin a Sudan, Khalid Osman, wanda yanzu aka tura aikin wucin gadi a wajen ƙasar da ake yakin, lamarin da wasu majiyoyi suka bayyana a matsayin wani abu mai kama da dakatarwa.
Babban jami’i na biyu da ya tsunduma cikin wannan cakwakiya kuwa shi ne, Mohammed Ali, wanda manajan yanki ne a wanna hukumar a Sudan, kuma ana tuhumarsa ne da hannu a ɓatan-dabo da man fetur kimanin lita 200 ya yi a birnin Kotsi.
Har zuwa yanzu dai Osman da Ali sun ki cewa uffan a game da wannan zargi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI