Wata rikitacciyar cuta da ba a gano wacce irin ba ce ta kwantar da dalibai mata 30 a jihar Sokoto da ke arewacin Najeriya.
Kwamishinan Lafiya na jihar Sokoto Dr. Abdurrahman Dantsoho ya shaida cewa, abun takaici ne yadda wannan abu ya faru a makaranta.
Dantsoho ya ce, an aika da jami'an lafiya 10 zuwa makarantar, kuma an dauki ruwa da ciyayi da ke makarantar don gudanar da gwaje-gwaje.
Kwamishinan ya kara da cewa, ya zuwa yanzu babu wanda ya rasa ransa sakamakon lamarin.