
A watan Afrilun shekarar da ta gabata, shugaban Sierra Leone Julius Maada Bio ya ayyana dokar ta-ɓaci biyo bayan kiraye-kiraye na a daƙile ayyukan masu amfani da wannan ƙwaya da ake kira kush, kuma ake ta’ammali da ita a ƙarin wasu ƙasashen yamacin Afrika 5.
Wannan ƙwaya na yin ta’asa a Serra Leone, inda yanzu haka take kashe gwamman mutane a duk mako, tare da aikewa da dubbai asibiti.
Akasari masu shan wannan ƙwaya, matasa ne masu shekaru 18 zuwa 25, kuma ƙwayar tana sa mai shan ta ya riƙa bacci a cikin tafiya, tare da faɗuwa yana dukan kansa ga bango, ko kuma ya shiga titin mota ko da kuwa motoci na wuce wa da gudu.
Amma rashin bayanai a game da sinadaran da wannan ƙwaya ta ƙunsa da ma asalinta ya sa yaƙi da ita ya kasance da baƙar wahala a cewar rahoton kungiyar, da ke bayyana kanta a matsayin mai yaƙi da aikata manyan laifuka ta Global Initiative.
An daɗe ana baza jita-jitar cewa ƙwayar ta ƙunshi duk wasu muggan ababe da suka haɗa da maganin ɓera, ƙasusuwan bil adama, amma binciken ƙungiyar Global Initiative zai taimaka wajen dakile tasirinta a kan masu ta’amali da ita.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI