An sanar da cewa an kai harin kunar bakin wake a arewa maso gabashin Najeriya lamarin da ya yi sanadiyar rayukan mutane uku.
Wani jami'in tsaron da ya nemi a boye sunansa ya shaidawa kanfanin dillancin labaran Anadolu da cewa a yankin Konduga dake jihar Borno wata yarinya dauke da bama-bamai ta kutsa cikin taron jama'a tare da tayar da bam din dake jikinta.
Jami'in ya kara da cewa a farkon bayanan da aka fara samu mutane 3 sun rasa rayukansu inda wasu 6 kuma suka raunana.
Duk da dai ba a dora alhakin harin akan kowa ba, kungiyar ta'addar Boko Haram ta jima ta na kai ire-iren harin a yankin.