Mutane 50 ne suka rasa rayukansu sakamakon kamuwa da wata cuta da ba a gama gano wacce iri ba ce a jihar Kogi da ke Najeriya.
Dan majalisar jihar mai wakiltar yankin Olamaboro, Ujah Anthony Alewo ya shaida cewar, wata cuta da ba a san wacce iri ba ce ta yi ajalin mutane 50 a yankin Etteh na jihar.
Alewo ya ce wadanda suka mutu na da shekaru tsakanin 25 zuwa 40, kuma wannan abu ne mai razanarwa.
Alewo ya kara da cewar an fara gudanar da bincike don gano ko wacce irin cuta ce.