A jihar Delta da ke kudu maso-kudancin Najeriya, wata cuta da ba a san wacce iri ba ce ta yi ajalin mutane 30 a mako guda.
Labaran da jaridun kasar suka fitar sun bayyana cewar a cikin mako dayan da ya gabata mutane 30 sun mutu a yankunan Ute Okpu da Idumusa sakamakon kamuwa da wata cuta da ba a gano wacce iri ba ce.
Mahukunta sun ce ana ci gaba da binciken gano musabbabin mutuwar mutanen, kuma kafin wasun su su mutu sun dinga yin amai, ciwon kai da kasalar jiki.