Joel Salifu wanda ya zama shugaban kwamitin yaki iftila’in ambaliyar ruwa na jihar Kogi na wannan shekarar 2024, ya na bayyana cewa,matakin da aka cimma ganin girman wannan iftila’in ya wuce karfin gwamnatin jiha. Ya kara da cewa, duk da matakan da gwamnatin jihar ta dauka na tunkarar ambaliyar ruwan a bana, halin da ake ciki a Edeha da sauran yankuna,lamarin da ban tsoro.
Wasu yankunan daya daga cikin jihohin Najeriya da suka fuskanci ambaliya AFP - AUDU MARTEYayin da ya jaddada cewa har yanzu ba a kai ga gano adadin dukiyoyin da suka lalace ciki har da filayen noma ba, mataimakin gwamnan ya nuna farin cikinsa da cewa kawo yanzu ba a rasa rayuka a cikin al’ummomin da abin ya shafa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI