Wasu mahara sun kai samame sansanonin shanu a Sudan ta Kudu

Wasu mahara sun kai samame sansanonin shanu a Sudan ta Kudu

Satar shanu, wadda aka alaƙanta da ƙarancin albarkatu na ɗaya daga cikin musabbabin rikice-rikice a tsakannin ƙabilun ƙasar, inda makamai su ka yi yawa sakamakon gwamman shekaru na yaƙe-yaƙe.

Maharan sun kai hare-hare a kan sansanonin shanu na yan ƙabilar Dinka Bor a ranar 31 ga watan Janairu, kamar yadda shugaban al’ummar yankin, Mayom Ateny,  ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters a yayin da ya ke bada ƙarin bayani a kan waɗanda su ka mutu da waɗanda su ka samu rauni a sansanoni 4 da aka kai samamen.

Olum Pole Pole Ataruk, kwamishinan ƙaramar hukumar  Magwi, inda lamarin ya auku, da Elia John Ahaji, ministan yaɗa labaran jihar Gabashin Equatorial, jihar da ƙaramar hukumar ta ke ba su ce uffan ba duk da buƙatar tsokaci da aka yi daga gare su.

Shanu na daga cikin mahimman alamu na dukiya a ƙasar Sudan ta Kudu, kuma a na bayar da su a matsayin sadaki ga iyayen budurwa.

Nicholas Haysom, shugaban ofishin Majalisar Ɗinkin Duniya a Sudan ta Kudu ya bayyana damuwa a kan yadda rikici ke ta’azzara a tsakanin makiyaya da al’ummomin Gabashin Equatoria.

Yaƙin basasa a Sudan ta Kudu a tsakanin shekarar 2013 zuwa 2018 ya haddasa mutuwar ɗaruruwan dubban mutane, kuma duk da cewa waɗanda su ka fara yaƙin su na zaman lafiya, an ci gaba da rikici tsakanin ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)