Wasu kasashen yankin Sahel za su kafa rundunar soji 5000 domin yakar ta'addanci

Wasu kasashen yankin Sahel za su kafa rundunar soji 5000 domin yakar ta'addanci

An shafe shekaru da dama wadannan kasashe na fama da hare-haren kungiyoyi masu ikirarin jihadi, abin da ya haifar da kalubale mai munin gaske ga ayyukan jin kai.

Ministan tsaron Nijar, Salifou Mody , a wata sanarwa da ya bayyana ta kafar talibijin, ya tabbatar da cewa, kasashen Burkina Faso, Nijar da Mali sun ce za su kafa runduna ta hadin gwiwa cikin makonni masu zuwa

Kasashe ukun da suka kasance wadanda Faransa ta taba yi wa mulkin mallaka, sojojin kasar ne suka hambarar da gwamnatocin farar hula yayin juyin mulkin da ya auku daga shekarun 2020 zuwa 2023.

Bayan juyin mulkin, kasashen uku sai suka nesanta kansu daga ‘uwargijiyarsu Faransa, inda a shekarar 2024 suka kafa wata kungiyar kawancen kasashen Sahel ta AES, da sunan bunkasa tattalinn arzikinsu da kuma magance matsalolin tsaro.

Wadannan kasashe dai, tsawon shekaru 10 su na fama da hare-haren kungiyoyin masu dauke da makamai, wadanda ake dangantawa da alaka da Al-Qaeda ko kuma kungiyar IS, amma gwamnatocinsu sun gaza kawo karshen matsalolin tsaron, duk da taimakon da suka samu daga sojojin Faransa.

Daga lokacin da suka kafa gwamnatocin soji, kasashen suka fara gudanar da ayyukan yaki da masu da’awar jihadi na hadin gwiwa, musamman ma a kan iyakokinsu da suka fi fuskantar hare-hare.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)