Wasu 'yan bindiga sun sake kai hari gidan kurkuku a Najeriya

Wasu 'yan bindiga sun sake kai hari gidan kurkuku a Najeriya

A jihar Abia dake kudu maso-gabashin Najeriya, wasu 'yan bindiga da ba a san ko su waye bai sun kai hari gidan kurkuku.

Labaran da jaridun kasar suka fitar na cewa, an kona gidan kurkuku na yankin Bende, kuma fursunoni da dama sun tsere.

A ranar 6 ga Afrilu ma an kai hari gidan kurkukun Owerri Babban Birnin jihar Imo dake wannan yanki inda fursunoni dubu 1,844 suka gudu, aka kuma kona motoci 50.

'Yan ta'addar a ware na IPOB na kai hare-hare makamantan wannan a kudu maso-gabashin Najeriya.


News Source:   ()