Wasu abubuwa sun fashe a kusa da Makarantar Asusun Ma'arif na Turkiyya da ke Mogadishu Babban Birnin Somaliya.
Mutane da dama sun samu raunuka sakamakon fashewar.
An kai wadanda suka jikkata zuwa asibiti, kuma ana zargin bam da ake ajje a gefen hanya ne ya fashi.
Babu wanda ya dauki alhakin kai harin.