Wasu abubuwa sun fashe a daya daga cikin tituna masu cinkoson jama'a da ke Mogadishu Babban Birnin Somaliya.
An bayyana jin karar harbe-harbe bayan fashewar.
Har yanzu ba a gama tantance ko an samu asarar rayuka ko jikkata ba sakamakon fashewar, an kuma sanar da tura jami'an sanda da ma'aikatan lafiya da dama zuwa yankin.