Wasu abubuwa sun fashe a Equatorial Guinea

Wasu abubuwa sun fashe a Equatorial Guinea

Mutane sama da 300 sun jikkata sakamakon fashewar wasu abubuwa a garin Bata na kasar Equatorial Guinea.

An samu fashewar abubuwa a kalla sau 4 a garin na Bata wanda shi ne cibiyar kasuwanci ta Equatorial Guinea.

Jaridun kasar sun sanar da mutuwar akalla mutane 20 da jikkatar wasu sama da 300 sakamakon fashewar abubuwan.

Gine-gine da dama sun lalace sakamakon fashewar.

Ministan Lafiya Guinea Salud ya shaida cewa, fashewar ta afku a sansanin soji na Nkoa Ntoma da ke garin Bata.

Salud ya bukaci ma'aikatan lafiya na sa kai da su je asibitin yankin Bata, kuma ya yi kira ga jama'ar yankin da su bayar da gudunmowar jini.

Har yanzu ba a san musabbabin fashewar abubuwan ba.


News Source:   ()