Wani sabon harin ta'addanci a Burkina Faso ya kashe manyan jami'an sojin ƙasar

Wani sabon harin ta'addanci a Burkina Faso ya kashe manyan jami'an sojin ƙasar

Bayanai sun ce ƴan ta’addar sun farwa sojojin ne a yankin Boungou, da ke lardin Tapoa na ƙasar.

 

Har yanzu babu cikakken bayani game faruwa lamarin daga mahukuntan ƙasar, sai dai kuma majiyoyi da dama daga rundunar tsaron ƙasar ta shaidawa sashen Faransanci na RFI cewa an sami asarar rayukan manyan jami’an tsaro a yayin wannan hari.

Bayanai sun ce baya ga asarar rayuka ƴan ta’addar sun tsere da manyan makamai da kuma tankokin yaƙi yayin fafatawar.

Wasu ƙarin bayanai da suka fayyace yadda lamarin ya faru, sun ce ƴan ta’addar sun yiwa sojojin kwanton ɓauna ne a kan hanyar da ta tashi tsakanin Ougarou da Boungou da ke gabashin ƙasar, hanyar da aka daina amfani da ita tun watan Nuwambar 2019, a sakamakon wani ƙazamin hari da aka kai kan masu haƙar ma’adanai.

Kai hari akan wannan hanya ba wani sabon abu bane, la’akari da yadda a baya ƴan ta’addar suka sha yiwa matafiya daga jami’an tsaro kwanton ɓauna suna kashe su.

Wata majiyar ta daban tace wasu daga cikin ƴan tawagar ne suka yanke shawarar bin hanyar a maimakon wadda aka tsara za’a bi a hukumance, dalili kenan da ƴan ta’addar suka hallaka su tare da kwashe kayan aikin su.

Wata ƙungiya da ke sanya idanu kan tsaro ta ce babu komai cikin wannan mataki illa ganganci da jami’an suka yi na bin hanyar, la’akari da sanin haɗarin da ke tattare da binta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)