Wani sabon harin Boko Haram a sansanin sojin Chadi ya kashe sojoji sama da 40

Wani sabon harin Boko Haram a sansanin sojin Chadi ya kashe sojoji sama da 40

Sanarwar da fadar gwamnatin Chadi ta fitar ta ce, mayakan Boko Haram sun kai gagarumin harin ne sansanin soji dake tsibirin Barkaram da ke yankin tafkin Chadi, a kudu maso yammacin ƙasar, ƙusa da iyaka da Najeriya.

Rahotanni sun ce da misalin ƙarfe 10 na ɗaren Lahadi mayakan Boko Haram suka kaddamar da farmakin, inda suka ci ƙarfin sama da sojoji 200 da ke wannan sansani, kamar yadda majiyoyin yankin suka bayyana.

Sanarwar fadar shugaban ƙasar ta tabbatar da mutuwar sojoji akalla 40, yayin da majiyoyin yankin suka ce adadin sojoji da suka mutu sun haura 60, tare da jikkatar wasu da dama.

Majiyoyin sun ce, maharan sun mamaye sansanin har zuwa wayewar garin Lititin, inda suka yi awon gaba da makamai da alburusai masu tarin yawa, bayan sun kona sansanin sojin.

Shugaba Mahamat Deby ya kai ziyara sansanin

Shugaban ƙasar Janar Mahamat Idriss Deby wanda ya kai ziyarar gani da ido sansanin da safiyar wannan Litinin, inda ya kaddamar da rundunar Haskanite da za ta yi farautar maharan a duk inda suke.

Wannan harin na zuwa ne makonni ƙadan bayan kawo ƙarshen rundunar hadin gwiwa ta ƙasa da ƙasa ta Operation Lake Sanity da ke yaki da Boko Haram a yankin Tafkin Chadi.

Kuma ga dukkan alamu tsuguni bata ƙare ba, duba da cewa har yanzu mayakan na ci gaba da kai hare-hare kasashen yankin, inda suka hana monoma da matsunta sakat.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)