Wani likita ya koka da tsarin yakar cutar kyandar biri daga hukumomin Burundi

Wani likita ya koka da tsarin yakar cutar kyandar biri daga hukumomin Burundi

 

A watan Satumba, Burundi da ke gabashin Afirka ita ce kasa ta biyu da ta fi fama da cutar kyandar biri a Nahiyar bayan Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo, inda Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa kyandar biri da aka sani da mpox ta shafi yara musamman.

 Wani likita dan kasar Burundi wanda ya nemi a sakaya sunansa ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa cewa, "halin da ake ciki dangane da annobar cutar mpox a Burundi na cewa da alama akwai rashin gaskiya da laifi." Kungiyoyi masu zaman kansu a kai a kai suna yin tir da danniya na siyasa da take hakkin dan Adam wanda ya sa mutane ke fargabar fitowa fili suna sukar hukumomi.

Cutar ta Mpox, wanda a baya aka sani da cutar kyandar biri, cuta ce da dabbobi masu kamuwa da cuta ke yadawa ga mutane amma kuma ana iya yadawa daga mutum zuwa mutum ta hanyar kusancin jiki kuma yana iya zama mai kisa.

 Likitan a Burundi ya ce jami'ai sun zabi su "boye ci gaban wannan annoba, wadda a halin yanzu ke shafar kusan kowane gundumomin kiwon lafiya a kasar", yana mai zargin gwamnati na hana ma'aikatar lafiya fitar da alkaluma. Wasu alkaluma daga kamfanin dillancin labarai na AFP ya ga alkaluman hukuma da suka nuna mutane 5,339 da ake zargi sun kamu da cutar daga ranar 25 ga watan Yuli zuwa 12 ga Disamba ,kashi 50 cikin 100 na masu dauke da cutar bas u samun kulawa da ta dace, kuma an gano cutar a yankuna 46 na gundumomin kiwon lafiya 49 na Burundi. Likitan ya ce "ba a shawo kan cutar ta mpox kwata-kwata a Burundi, akasin haka," in ji likitan, yana mai cewa a duk kullum ana gano mutane 10 a kullum

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)