Wani kamfanin haɗa magunguna zai taimawa wasu ƙasashen Afrika da rigakafin ƙarambau

Wani kamfanin haɗa magunguna zai taimawa wasu ƙasashen Afrika da rigakafin ƙarambau

Tun bayan da WHO ta ayyana dokar ta ɓaci kan cutar ta ƙyandar biri da ke ci gaba da yaɗuwa a Congo ne hankula suka karkata kan cutar da ɗaukar matakan yaƙi da ita, ko da ya ke har yanzu ba a iya samarwa cutar rigakafin kai da kai ba, face na cutar ƙaranbau da ake ci gaba da amfani da shi don yaƙarta duka da cewa ƙasashen Amurka da Japan sun shige gaba wajen fara aikin samar da rigakafin a kamfanonin sarrafa magungunansu.

Bayan alƙwarin da kamfanin na Emergent BioSolution da ke Amurka ya yi, Congo ta bayyana cewa nan da mako mai zuwa za ta karɓi rukunin farko na alluran rigakafin cutar daga Amurka da Japan don yaƙi da ƙyandar biri, a wani yanayi da ake ganin ƙaruwar alƙaluman waɗanda ke harbuwa da cutar a sassan ƙasar.

Ma’aikatar lafiyar Congo ta ce an samu ƙaruwar mutane 700 da suka harbu a ƴan tsakanin nan haka zalika alkaluman wadanda cutar ta kashe ya kai 570 daga 548 a baya.

Ƙaruwar alƙaluman na zuwa a dai dai lokacin da hukumar lafiya ta duniya WHO ke kwantar da hankulan jama’a ta hanyar nesanta cutar ta ƙyandar biri da kasancewa sabuwar cutar COVID.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Hulda da mu

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI


News Source:   RFI (rfi.fr)