Wasu mutane ne dauke da makamai suka je gidan Atiana Serge Oulon, darektan kamfanin a watan Yuni kuma suka yi awun gaba dashi a wata mota kirar bas kamar yadda kungiyar ƴan jarida ta duniya ta bayyana.
Rahoton kungiyar ta reporters without borders ya bayyana cewa bayan akalla sa’o’i biyu da sace daraktan sai wasu kuma daga bisani suka ziyarci gidan a matsayin jami’an tsaro yayin da suka kwace na’urarsa ta kwamfuta da kuma wayarsa.
Dama dai Shugabannin sojojin kasar ta Burkina Faso da suka kwace mulki a shekara ta 2022, na shan suka daga kungiyoyin kare hakkin bil adama kan matakan da suka dauka da sunan tsaron kasa.
Kungiyoyin kare hakkin bil adama na Amnesty International da Human Rights Watch (HRW) sun zargi gwamnatin mulkin sojin kasar da kame wasu daga cikin masu sukarta aiki, tare da rashin mutunta kungiyoyin faraen hula.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI