Harin wanda shi ne mafi muni da aka kai a kasar tun a cikin shekara 2021, an kaishi kan dakarun runduna yaki da ta’addanci ta Mirador dake aikin tabbatar da tsaro a iyakan Nijar da kuma Burkina Faso.
Wasu manyan jami’an tsaro sun ce harin ya haddasa mumunar barna a bangaren sojoji yayin da ake cigaba da tattara bayanai daga wadanda suka ketara rijiya da baya.
Yi zuwa yanzu gwamnati bata fitar da wasu alkalumma a hukumance dangane da adadin sojin suka mutu a harin.
Shugaban kasar Patrice Talon, ya fada a wata hira cewa, ‘yan ta’adda dake cin karansu babu babbaka a iyakokin kasar na cigaba da kalubalantar jami’an tsaron duk da kokarin da suke bayer wa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da muKu saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI